15 Yuni 2020 - 07:52
Amurka : Shugabar ‘Yan Sanda Atlanta Ta Yi Murabus, Bayan Kisan Wani bakar Fata

Shugabar ‘yan sandan yankin Atlanta babban birnin jihar Georgia a Amurka, Erika Shields, ta yi murabus bayan da wani dan sanda ya sake kashe wani bakar fata ta hanyar barbin bindiga a kasar.

(ABNA24.com) Shugabar ‘yan sandan yankin Atlanta babban birnin jihar Georgia a Amurka, Erika Shields, ta yi murabus bayan da wani dan sanda ya sake kashe wani bakar fata ta hanyar barbin bindiga a kasar.

Magajiyar birnin na Atlanta ce Keisha Lance Bottoms, ta sanar da murabus din shugabar ‘yan sanda yankin na nan take, bayan shafe shekaru 20 tana shugabancin ofishin.

Lamarin ya haifar da barkewar wata zanga zanga ta kyammar nuna wariyar launin fata da cin zarafin da ‘yan sanda ke yi wa bakaken fata a kasar.

Rahotanni daga Amurka sun ce masu zanga zanga sun yi ta kone kone a ranar Asabar inda har suka kone wani gidan abinci da kuma toshe wata babbar hanya a yankin.

Tashar talabijn ta rawaito cewa an kama mutane da dama yakin tarzomar data biyo bayan kisan bakar fatar dan shekaru 27 mai suna Rayshard Brook.

Wannan dai na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan tarzomar data barke a manyan biranen Amurka, biyo bayan kisan George Floyd, shi ma bakar fata da wani da sanda farar fata ya danne ma wuya da guiwa, har na tsawon kimin minti 9, wanda kuma hakan ya yi silan mutuwarsa.



/129